Akwai hanyoyi da dama na sarrafa kaza ko grilled chicken. A yau na kawo maku hanya mai sauki sannan mai dadi, matukar kuka gwada za ku ji dadinsa.
Abubuwan bukata:
1- 1 big chicken
2- 1 teaspoon honey
3- 1/2 teaspoon parsley flakes
4- 1/2 teaspoon black pepper
5- 1 cup pepper mix
6- 1/2 onion
7- 1 teaspoon ginger and garlic paste
8- 2 tablespoons maggi powder
9- 1/2 teaspoon salt
10- 1 tablespoon oil
11- 1 sachet chicken seasoning
13- 1 tablespoon dakakken yaji
Yadda ake yi:
1- ki wanke kaza tas, ki zuba a pot, ki saka albasa, dandano, ginger and garlic paste, sai ruwa kadan, ki bari ta dahu amma ba tubus ba. Sai ki samu kyakkyawan bowl dinki, ki zuba pepper mix wanda sai da kika tafasa shi da kayan kamshi sannan kika markada, sai ki saka zuma, parsley, da chicken seasoning

2- ki saka mai, black pepper, dakakken yaji, sannan ki motsa da kyau komai ya hade.

3- then ki dauko tafasasshiyar kazarki ki tsoma a wannan hadin da kika yi, ki tabbatar komai ya kama ta sannan ki saka a fridge na awa daya zuwa awa biyu. Daga nan sai ki jera a kan baking tray ki gasa na minti arba’in zuwa awa daya.
