Mu koyi yadda ake gashin hakarkari ko awazun rago cikin sauki. Wannan gashi ne mai dadi da kuma ingancin gaske. Uwargida a gwada a bamu labari!
Abubuwan hadawa
- Awazunki (hakarqari) na rago mai kyau kaman yadda ki ka ga hotonnan
- Kayan kamshi (habbatussauda, busashshiyar na’a-na’a, garin thyme)
- Mai
- Maggi
- Yaji (ga me buqata)
- foyil paper (foil paper)
- Oven
Yadda ake hadawa
- Da farko ‘yar uwa za ki hada mai, da kayan kamshi, da maggi, da yaji ki cakude wuri guda, ki shafe jikin awazun gaba da baya, sannan ki nannade a foil paper ki sa a oven.
- Za a bar shi cikin oven ya gasu na kimanin minti talatin zuwa arba’in.
- Sannan ki ciro ki bude foil din ki maida shi cikin oven din a bude na kimanin mintuna goma sha biyar! Bayan nan sai a ciro a yayyanka shi sala sala!
Bayan an gasa shi a bude na tsawon minti 15
Wannan ba gashi ne na wasa ba! Sai an gwada akan san na kwarai!!!