Skip to content

Yadda ake gashin hakarkari/awazun rago

Share |
Yadda ake gashin hakarkari_awazun rago

Mu koyi yadda ake gashin hakarkari/awazun rago cikin sauki. Wannan gashi ne mai dadi da kuma ingancin gaske. Uwargida a gwada a bamu labari!

Abubuwan hadawa

  1. Awazunki (hakarqari) na rago mai kyau kaman yadda ki ka ga hotonnan
  2. Kayan kamshi (habbatussauda, busashshiyar na’a-na’a, garin thyme)
  3. Mai
  4. Maggi
  5. Yaji (ga me buqata)
  6. foyil paper (foil paper)
  7. Oven

Yadda ake hadawa

  1. Da farko ‘yar uwa za ki hada mai, da kayan kamshi, da maggi, da yaji ki cakude wuri guda, ki shafe jikin awazun gaba da baya, sannan ki nannade a foil paper ki sa a oven.
  2. Za a bar shi cikin oven ya gasu na kimanin minti talatin zuwa arba’in.
  3. Sannan ki ciro ki bude foil din ki maida shi cikin oven din a bude na kimanin mintuna goma sha biyar! Bayan nan sai a ciro a yayyanka shi sala sala!

Bayan an gasa shi a bude na tsawon minti 15
Wannan ba gashi ne na wasa ba! Sai an gwada akan san na kwarai!!!

Add to Lists (0)
ClosePlease loginn

No account yet? Register

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page