Mu koyi yadda ake gasa tsokar naman sa mai armashi. Wannan gashi ne mai dadi da kuma ingancin gaske. Uwargida a gwada a bamu labari!
Abubuwan hadawa
- Tsokan nama sa zalla
- Kayan kamshi (habbatussauda, busashshiyar na’a-na’a, garin thyme, da maggi)
- Mai
Yadda ake hadawa
1. Ki dauko namanki tsoka zalla ki yanka fala fala kaman fefa. Kamar yadda za ku gani a hoton da ke zuwa a kasa.
2. Abu na gaba shi ne, ki kawo kayan kamshi da muka lissafa a samannan sai ki hade su a waje guda sannan ki sa mai ki cakuda.
3. Sai ki bi ki shafe wannan nama da ki ka ajiye a gefe da wannan hadin kayan kamshin. Ki tabbatar kin shafe nama sosai da kayan kamashinnan.
4. A daura abin tuyan kwainki a wuta wato frying pan sai ki sa mai kadan sannan ki dora naman a kai. Idan gefe daya ya yi sai ki juya dayan gefen.
5. Da namanki ya yi sai ki yanyanka shi a tsaye Kamar yatsu. Ga hoton yadda na yi nawa ku duba a kasa.
Karin bayani
Wannan gashin tsokan sa ina amfani da shi a girke-girke daban-daban. Kin ga ni in na yi kalan gashin nan, nakan sa shi cikin salad, ko in sa cikin shinkafa, da taliya da sauransu! Abin ba a cewa komi, sai angwada!