Skip to content

Yadda ake gasa kifi tarwada

Share |
Yadda ake gasa kifi tarwada
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Mu koyi yadda ake gasa kifi tarwada cikin sauki, abubuwan hadawa guda goma, matakai guda shida tare da ‘yan dabarun yadda zai inganta.

Abubuwan hadawa

  1. Kifi tarwada
  2. Spices (citta, tafarnuwa, kanumfari)
  3. Man gyada
  4. Foil paper
  5. Kaskon suyan kwai mai fadi (ko oven)
  6. Maggi star
  7. Tattasai
  8. Attarugu
  9. Albasa
  10. Tumatir

Yadda ake hadawa

  1. Ki wanke kifinki da toka tsaf, saboda toka na cire wannan yaukin nan na jikin kifi tarwada.
  2. Ki ajiye a gefe kada ki yayyanka, ya tsane ruwansa tsaf.
  3. Ki yi jajjagen tattasai da attarugu da citta da tafarnuwa da kanamfari.
  4. Sai ki hade jajjagen nan da maggi sannan ki zuba mai a ciki, ki cakuda, ki shafa a jikin kifinki da ya tsane ciki da bai. Ki tabbatar ko ina ya ji, sai ki rufe ki ajiye kamar na minti 30 a fridge. 
  5. A nan sai ki yayyanka albasa da tumatir rawun-rawun (round shape).
  6. bayan kin kammala komai na hadin da yanke-yanken, sai ki dauko foil paper ki shimfide shi a kan frying pan din (kaskon suya), sai  ki daura kifin a kai, ki jera albasa da tumatir sannan sai ki nannade ki rufe ko ina da foil din. Ki daura a kan wuta. In gefe daya ya gasu sai ki juya dayan gefen tare da foil din yadda  kifin ba zai rabe ko ya karairaye ba. In kuma oven gare ki cikin sauki sai ki kunna sama da kasa sai su gasu lokaci daya.

Hikima cikin wasu abubuwan

  1. Wanke kifi tarwada da toka yafi saurin cire wannan yaukin da karnin kifin.
  2. Barin kifin da kayan kamshi da maggi a jikinshi kamar na minti 30 kafin gashi na sa shi ya kama jikin kifin ya shige ko ina da ina, dandanon ya fito da kyau. Wannan shi ne ake kira ‘marinade’ a turance. 
  3. Nannade kifi a cikin foil paper yana sa sauki wurin juyawa sannan kifinki ba zai dagargaje ba, ba kuma zai kama ba balle ki sha wahala wurin juyawa ko kuma kwashewa.

Zamu so mu ji comment na ku game da wannan recipe, yin hakan zai kara mana kwarin gwuiwa wajen kawo muku wasu recipes masu inganci gaba.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×