Uwargida da amarya ku koyi yadda ake fruit salad cikin sauki, abubuwan hadawa guda bakwai, matakai guda uku.
Abubuwan hadawa
- Abarba
- Kankana
- Ja da koriyar tuffa
- Inibi
- Fiya (pear)
- Sugar
- Filabo na abarba (pineapple flavour)
Yadda ake hadawa
- Ki yayyanka duk kayan marmarin da muka ambata kanana sai ki ajiye agefe.
- Sai ki samo abarba ki niqa ta ablender da sugar ki tace kidan sa filabo na abarba ki zuba a ciki.
- Ki gauraya sai ki juye hadin a kan yankakkun kayan marmarinki sai ki sa a cikin fridge yayi sanyi.
‘Yanuwa a sha dadi lafiya. Bazan ce komi ba sai na ji comments dinku. kada kubari a baku labari.