Ga yadda ake fried rice mai kaza mu koya ‘yanuwa. Wannan recipe ne na fita kunya da tsara, uwargida ki gwada ki bani labari.
Abubuwan hadawa
- Tafasashshe shinkafa (Perboiled rice)
- Tarugu (ba dole ba)
- Shredded chicken (ficinennen naman kaza) Ko hanta
- Madarar kwakwa
- Albasa (ki yanka )
- Karas da koren wake (green beans) – ki yankasu
- Curry powder
- Maggi
- Gishiri domin dandano
- Butter
- Kayan kamshi
- Peas (ina amfani da na gwangwani)
- Ruwan silalenki (Kaza)
Yadda ake hadawa
- Ki dauko karas da koren wake ki sa su a kwano sai ki dauko baking powder ki sa ki juya su, ki sa ruwa akan wuta idan ya tafasa ki zuba a ciki sai ki rufe na dan wani lokacin haka idan ya yi laushi sai ki zuba ruwa akai sai ki tace a matsani ki ajiye a gefe
- Peas (na kanyi amfani dana gwangwani ya fi kyau da girma) za ki fafe bakin gwangwani ki juye shi a dan wani kwano mai zurfi sai ki sa ruwan zafi ki isashshen ruwa akai sai ki tace a matsani ki barshi ya tsane.
- Ki sa tukunya akan wuta ki sa butter ki a ciki, har sai ya narke, ki sa tarugunki da albasa ki a ciki ki soya sama sama. Sai ki zuba su maggi da curry da ruwan silalenki a ciki tare da madarar kwakwanki daidai yanda zai dafa mi ki shinkafarki, ko kidan kara ruwa Yanda zai dafa miki shinkafa ki (idan kin ga ruwan silalenki da Madarar kwakwa bazai yi ba).
- Anan sai ki rufe shi ya tafaso (idan ki na so za ki yi iya cire tarugu dana sa a ciki, nima dan bana son abinci yamin salam ne) Kuma kadan za ki sa yanda bazai fito sosai ba.
- Ki dauko tafasashshiyar shinkafan naki ki sa a ciki sai ki juya.
- Ki sami foil paper ko leda babba ki sa ki rufe saman shinkafan da shi, sai ki dauko marfin tukunya ki rufe idan ya nuna sai ki sauke ki sa ki ajiye a gefe.
- Ki sa tukunyarki da baya kamawa (non stick pan) a wuta tsaka tsakiya (medium heat) ki sa butter ki a ciki har sai ya narke.
- Ki dauko shredded chicken Ko hanta ki sa ki na dan juyashi a hankali.
- Sai ki dauko su karas, da koren wake da peas naki ki sa a ciki ki juya su.
- Ki dauko dafaffafiyar shinkafarki ki sa a ciki ki na juyawa a hankali, haka za ki yi da sauran kayan hadinki har ki gama dashi.
Za ki iya sa soyayen plantain da kuma soyayyen kifi akai. A ci dadi lafiya
Akoya min yadda ake fara da rice da kuma yadda ake jar miya