Skip to content

Yadda ake fluffy vanilla pancake

Share |
Yadda ake fluffy vanilla pancake
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake fluffy vanilla pancake. Domin hada wannan fluffy vanilla pancake mai taushi za a bukaci 8 ingredients ne da kuma steps biyar!

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi daya
  2. Baking powder karamar cokali daya
  3. kwai daya
  4. Suga babban cokali uku
  5. Madarar gari babban cokali hudu
  6. Mai babban cokali shida
  7. Ruwan dumi kadan
  8. Vanilla flavour kwatan karamin cokali

Yadda ake hadawa

  1. Ki samu roba ki fasa kwai, ki sa mai sai ki juya su, ki zuba ruwan dumi (lukewarm water), suga, sai madarar gari, baking powder, vanilla flavour ki yi mixing na su komai ya hade.
  2. Sai ki dauko filawa ki zuba ki sake whisking komai ya hade. Ki rufe ki barshi na minti goma.
  3. Bayan minti goma sai ki daura pan akan wuta (ko non stick ko ba non stick ba zaiyi). In non stick ne babu bukatar saka mai, in kuma ba non stick ba ne sai ki sa mai kadan, ki rage wutan sosai ki barta a low temperature,
  4. Bayan kinsa mai sai ki dauko ludayi ko wani abun ki diba kullin ta ki ki zuba bayan wani dan lokaci za ki ga yana tashi har zai zo ya fara yin bubbles haka (bulali) sai ki juya dayan side din,
  5. Bayan kin juya still za ki ga yana tashi, ki bar shi na dan wani lokaci sai ki sauke. Ki sake diba kullin ta ki ki bi yadda ki ka yi da farko har ki kare kullin.

Karin bayani

  1. Idan ki na son pancake na ki ya zama fluffy to ki samu baking powder mai kyau, sannan ya na da kyau ki yi amfani da ruwan dumi gun dama kullin ta ki.
  2. Ki dama kullinki da kauri kada ya yi ruwa shi ne zai baki even shape wa duk pancake na ki kuma ya yi kyau.
  3. Sannnan bayan ya yi bulali (bubble) kin juya dayan gefen din kada ki yi masa aikin karfi (applying presssure) ko ki danne shi, in ki ka yi haka za ki hana shi ta shi, zai kwanta.
  4. Idan za ki ci da onion sauce ne ki rage suga din kada ki sa cokali 5 (Tbsp) ki sa cokali 3(Tbsp)
  5. Dadin dadawa kuma wutanki ya zama ya na low har ki gama gasa shi.

Za ki iya cin pancake da tea, melted chocolate, chocolate sauce ko kuwa da onion sauce, ko dai ma duk abinda ki ke sha’awa.

. Idan da sauce kikeson ci sai kisa Rabin COKALI da gishiri aci.

Yadda ake chocolate sauce

Ki tanadi cocoa powder babban cokali biyu, madarar gari babban cokali uku, sugar babban cokali uku sai ruwa kadan ki dama sai ki ci da pancake.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×