Skip to content

Yadda ake faten wake da doya

Share |
yadda ake faten wake da doya
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Uwargida mu koyi yadda ake faten wake da doya. Wannan faten wake da doya din yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Wake (kofi daya)
  2. Doya (gwargwadon bukata)
  3. Attarugu 3
  4. Tattasai 2
  5. Albasa 2
  6. Kifi busasshe
  7. Manja
  8. Alayyahu
  9. Maggi 8
  10. Kori
  11. Tafarnuwa
  12. Gishiri

Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida ki gyara wakenki ki dora a wuta ki bashi lokaci don yanuna.
  2. Sai ki fere doyarki ki yanka kanana ki wanke ki ajiye a gefe.
  3. Sai ki gyara kifinki ki wanke ki ajiye agefe shima
  4. Sai ki yanka alayyahonki yanka manya, sai ki wanke ki ajiye agefe.
  5. Har ila yau, sai ki jajjaga kayan miyanki harda tafarnuwa ki ajiye agefe.
  6. Sai ki duba wakenki idan yayi laushi sai ki tace amma kar yayi laushi sosai.
  7. Sai ki dora tukunya a wuta ki sa manjanki ki yanka albasarki yadan fara soyuwa, sai ki zuba kayan miyanki idan ya soyu saiki zuba ruwa yadan tafasa.
  8. Sai ki zuba doyarki ki kawo maggi da gishiri da kori da kifi ki zuba ki rufe yayi kamar minti biyar sai ki zuba wakenki ki rufe yayi minti ashirin.

Idan yayi daidai saukewa sai ki zuba alayyahonki da yankakkiyar albasa ki juya sosai, sai ki sauke ki zuba a kwanonki mai kyau.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×