Ga yadda ake faten shinkafa na zamani da surkin gargajiya.
Abubuwan hadawa
- Shinkafa
- Alaiyaho da yakuwa (ki gyara ki yanka su, ki wanke da gishiri)
- Albasa mai lawashi (ki yanka)
- Maggi (ya danganta da irin dandano ki)
- Tarugu (ki jajjaga)
- Albasa (ki yanka)
- Manja mai kyau (ki soya)
- Gyadar miya zaki dakata (optional)
- Dafaffafen nama ko kifi banda (ya danganta da irin wanda kike so)
Yanda ake hadawa
- Da farko ki sa tukunyanki akan wuta ki sa ruwa yanda zai isheki ki dafa shinkafar ki. Har ya danyi ruwa ruwa (tunda fate akace) Saiki wanke shinkafarki ki zuba a ciki ki barshi yayita tafasa har sai kinji ta fara laushi.
- Sai ki dauko tarugu ki sa ki kawo maggi, nama ko kifi, curry, kayan kamshi da gishiri ki sa daidai dandano da zai miki.
- Ki dauko manja ki sa, sai ki kawo ganyen lawashi ki zuba a ciki, daga karshe kuma ki dauko gyada ki zuba sai ki juya a hankali. Sannan ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin (amma ki na juyashi a hankali nadan wani lokaci) har sai komai ya nuna.