Skip to content

Yadda ake farfesun kifi banda

Share |
Yadda ake farfesun kifi banda
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake farfesun kifi banda cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi bakwai da kuma steps biyar.

Abubuwan hadawa

  1. Kifi banda (ki tabbbatar marar tsutsa ne)
  2. Kayan kamshi
  3. Maggi
  4. Tarugu (ki yanka)
  5. Albasa (ki yanka)
  6. Gishiri kadan
  7. Mai

Yadda ake hadawa

  1. Ki samu kifin ki mai kyau marar kasa da tsutsa ki wanke shi tas (idan kin tabbatar kifin ki mai kyau ne ba sai kin bare ba). Sai ki sami ruwan zafi ki zuba a kai ki rufe nadan wani lokaci.
  2. Sai ki daura tukunya a kan wuta, zuba mai kadan ki yanka albasa ki soya sama sama sai ki kawo tarugu (wanda ki ka jajjaga) ki raba kashi 3 sai ki zuba kashi 2 a cikin mai da ke kan wuta ki soya sama sama. Ki kawo kayan kamshi,maggi iya dandanon da zai mi ki da gishiri kadan ki sa ki juya.
  3. Sai ki tsane kifi ki a cikin ruwan da ki ka jika shi (idan ki na so za ki iya amfani da ruwan jikakken kifi) ko kuma ki sa ruwan zafi akan kayan miyan ki daidai yanda zai isheki ko ki ke son roman ya kasance.
  4. Sai ki kawo kifinki ki sa a ciki ki juya ki rufe nadan wani lokaci ya yi laushi.
  5. Daga karshe ki kawo ragowar tarugun ki ki sa a ciki ki juya ki barshi yadan turaru sai ki sauke ki zuba a kwano. A ci dadi lafiya

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake farfesun kifi banda”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×