A yau kuma tafe muke da yadda ake farfesun dankali, wannan romon dankalin cikin sauki za ki hada shi, biyo mu a hankali dan ganin namu salon.
Abubuwan hadawa
- Dankali
- Attarugu
- Tattasai
- Albasa
- Maggi
- Curry
- Mai
- Gishiri
Yadda ake hadawa
- Za ki tafasa dankalin da dan gishiri.
- Za ki markada kayan miyarki kisa a tukunya, sai kisa mai kadan ki soya kamar minti biyar.
- Sai ki sa ruwa rabin kofi da maggi, da gishi, da kuma curry
- Sai ki zuba dankalinki, ki tafasa kawai sai ki barshi kamar minti sha biyar.
- Sai a sauke a ci da maigida da yara.