Skip to content

Yadda ake egg vegetable soup

Yadda ake egg vegetable soup
5
(3)

Ku koyi yadda ake egg vegetable soup. Wannan soup ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!

Abubuwan hadawa

  1. Alaiyaho (ki yanka)
  2. Ganyen ugu (ki yanka)
  3. Tarugu da tattasai (ki jajjaga)
  4. Kwai dafaffafe (ki yanka kanana)
  5. Albasa(ki yanka)
  6. Mangyada
  7. Lawashi (ki yanka)
  8. Maggi
  9. Kayan kamshi

Yadda ake hadawa

  1. Daura tukunyanki akan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama, sai ki kawo tarugun, tattasai da ki ka jajjaga ki sa a ciki ki juya ki soya sama sama, kawo kayan kamshi, maggi da gishiri ki sa iya dandano da zai miki ki juya rufe nadan wani lokaci.
  2. Sai ki kawo ganyen alaiyaho dana ugu, da lawashi ki sa ki juya ki kara albasa ki kawo dafaffafen kwanki ki zuba a ciki ki juya sai ki dauko murfi ki rufe tukunya ki nadan wani lokaci.
  3. Anan sai ki sauke ki zuba akan abinci. Ana iya cin wannann miya da taliya ko shinkafa ko couscous da dai sauransu. A ci dadi lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×