Ga yadda ake doya da kwai da duk muke so. Karanta ku gwada!
Abubuwan hadawa
- Doya
- Kwai
- Man gyada
- Tarugu
- Gishiri
- Koren tattasai
- Albasa
- Dakakken yaji me dadi (yaji Maggi da Kayan kamshi)
Yadda ake hadawa
- Ki sami doyarki mai kyau ki fere sai ki wanke ki daura ta kan wuta ki sa gishiri, sai ki rufe har sai ya nuna ki sauke ta, ki cire ta cikin ruwan da kika dafa ta kisa a matsami ya tsane ya sha iska (idan doya ta huce yafi kama kwai jikin sa).
- Sai ki dauko tarugunki, koren tattasai da albasa ki wanke sai ki yanka su kanana.
- Ki sami kwano ki fasa kwanki a ciki, ki buga shi sosai, sai ki kawo su albasa, koren tattasai, da tarugun da kika yanka ki sa a ciki, sai ki buga shi sosai (idan ki na so zaki iya sa maggi amma ni ban cika sa maggi ba don ya na tsinka kwai).
- Sai ki daura man gyada a kan wuta idan ya yi zafi sai ki dauko doyanki ki na tsomawa cikin kwanki ki na soyawa a cikin mai har sai ya soyu.