Skip to content

Yadda ake danwake

Share |
Yadda ake danwake
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake danwake. Wannan danwake mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!

Abubuwan hadawa

  1. Filawa
  2. Garin alabo (garin rogo)
  3. Kuka
  4. Kanwa
  5. Dakakken yaji
  6. Maggi
  7. Albasa
  8. Koren tattasai
  9. Tumatur
  10. Jan tattasai
  11. Man gyada (ki soya da albasa)

Yadda ake hadawa

  1. Dauko kanwa ki jikashi ya jiku, ki barshi ya kwanta sai ki tace ki ajiye a gefe.
  2. Dauko albasa, tattasai, koren tattasai da tumatur ki wanke ki yanka su gu daya ajiye a gefe.
  3. Ki daura tukunya akan wuta ki sa ruwa (yanda zai isheki dafa danwakenki). Ki dauko kwano babba ki tankade filawa da garin alabo (dan daidai za ki sa alabon, filawa tafi yawa) ki sa kuka, ki sa ruwan kanwa da ruwa (kar ya yi ruwa ruwa kuma kar ya yi tauri),ki kwaba shi da muciya (amfanin kwabawa da muciya ya fi sa danwake ya yi sumul sumul) ajiye a gefe.
  4. Idan ruwan ki na kan wuta ya tafasa, ki bude ki fara jefawa a ciki, ki na jefawa bayan wani dan lokaci ki na dan juyashi a hankali (amfani yin hakan dan kar su manne a jikin juna kuma don ki sami sararin sa wasu), haka za ki yi har sai kwabin danwake ya kare.
  5. Sai ki rufe nadan wani lokaci amma ki tabbata ki na kusa don kar ya yi bori, idan ya nuna sai ki sami wani babba kwano ki zuba ruwan dumi ki na kwashewa da matsani ki na zubawa a cikin ruwan har sai kin gama kwashewa.
  6. Daga karshe, sai ki sake tsanewa da matsami ki sa a plate ki kawo yankakken su tattasanki ki sa a gefe ki zuba yaji da man gyadanki. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake danwake”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×