Ku koyi yadda ake dankali da kwai mai ban sha’awa ga dadi ga kuma kyau. Ana bukatan steps shida ne domin hada wannan dankali da kwai din.
Abubuwan hadawa
- Dankalin turawa
- Kwai
- Man gyada
- Tarugu
- Albasa
- Gishi kadan
Yadda ake hadawa
- Ki sami dankalinki na turawa ki fere (kada ki yanka su) ki wanke sai ki daura akan wuta ki sa gishiri kadan. Sai ki barshi akan wuta na dan wani lokaci har sai ya nuna sai ki tsane a matsani idan ya sha iska sai ki dauko wuka ki yankashi iya girman da kike so. Ajiye a gefe.
- Dauko wani kwano daban ki fasa kwanki a ciki sai ki yanka albasa tarugu a ciki, sai ki kawo dan kayan kamshi (kamqr garin citta) ki sa, gishiri ki sa kadan sai ki buga shi sosai, ajiye a gefe.
- Daura kasko akan wuta ki sa man gyada, idan ya yi zafi sai ki dauko dankalinki ki na tsomawa a cikin ruwan kwan (za ki iya amfani da cokali dan kwan ya zauna sosai a jikjn dankalin) ki na sawa a cikin manki dake kan wuta (ki tabbatar man ya yi zafi).
- Ki bar shi nadan wani lokaci sannan ki juya dayan gefe, idan ya soyu sai ki kwashe ki sa a matsani ki bari man dake jiki ya tsane ki zuba a plate.
- Sannnan ki dan yi sauce mai dadi ki sa a gefe ko ki yanka albasa, da tarugu da su tumatur ki sa a gefe. Aci dadi lafiya.