Uwargida ga yadda ake dankali a cikin kwai da plantain. Wannan recipe na bukatan kayan hadi shida da kuma steps uku.
Abubuwan hadawa
- Dankalin turawa
- Kwai
- Maggie
- Curry
- Lawashi
- Mai
Yadda ake hadawa
- Ki fere dankali ki wanke haka kada ki raba, ki bar su guda guda. Ki daura tukunya a wuta ki sa ruwa da gishiri kadan sai ki zuba dankalinki ki bari ya nuna (amma kada ki bari ya fara fashewa).
- Sai ki sauke, bayan kin sauke sai ki samu karamar bowl ki fasa kwai, ki sa maggie, curry da lawashi ki buga.
- Ki daura mai a wuta in ya yi zafi sai ki na sawa a cikin kwai ki na soyawa (idan man ki bai yi zafi ba kwan ba zai kama jikin dankali ba).
Soyayyiyar Kwai da plantain
Ki fasa kwai a cikin roba, ki sa tumeric (kurkur), Maggie, lawashi, attarugu ki kada sannan ki soya.
Plantain din kuma ki rage kullin kwan ki soya da shi.