Ku karanta yadda ake danderun nama na asali daga Borno. Muna jin labarin danderun Maiduguri, yau dai ga shi a tafin hannunku. Sai an gwada…
Abubuwan hadawa
- Nama
- Albasa
- Attarugu
- Yaji
- Maggie
- Gishiri
- Mai
- Spice da ki ke so ko ki ke da shi (na yi amfan da black pepper, nut meg da coriander powder)
- Seasoning da ki ke so
- Tafarnuwa
Yadda ake hadawa
- Za ki wanke naman ki sai ki ajiye agefe. Ki daka nutmeg da black pepper in ba ki da dakakkiya.
- Ki nemi roba ki sa mai, attarugu, albasa, yaji, onga classic, tafarnuwa, maggie, spice and seasoning, sai ki zuba su nutmeg na ki da ki ka daka a cikin bowl din ki hada su.
- ki dauko naman ki kisa wuka kidan tsatstsaga ta. Sannan ki dauko marinate naki na roban ki shafa ko ina a jikin naman kowani lungu lungu.
- Bayan kin gama marinating sai ki nemi tukunya ki sa ruwa sai ki sa murfin kwano a ciki sannan ki sa denderun na ki.
- ki nemi paper foil/ ko normal paper ki rufe naman naki. Ki barshi akan wuta ya nuna.
Karin Bayani
- Ba’a juya danderu hakanan zai nuna a low temperature. Yawanci a sallah muna yi da darraddare mu barshi a kasan garwashi gari ya waye
- Yawanci ana amfani ne da wuyar rago ko side na rago ko kuma cinyar rago wajen danderu.
- Idan danderu ta nuna ki na tabawa za ki ga namar na barin jikin kashin alamun ya yi kenan.
- Kisa enough kayan hadi gun yin danderu su Maggie da sauransu. Akwai wani abu daya da danderu in ba ki sa enough maggie ba in ya nuna za ki ji taste din ya koma baya, to maggie bai jiba. Saboda Hala, ki sa Maggie da seasonings suji amma kuma kada ki cika sosai.
Wow
Nagode da wannan bayani. Amma ina son karin bayani, ruwan sa za a sa a tukunyar kamar yaya za a sa shi. Sannan naman da ke cikin foil a cikin ruwan za a sa ko za ayi yadda akeyin burabusko ne wato steaming ne zai dafa shi.
Anayin shi kamar yadda tukunyar dambu ta ke ne, wato a dora naman akan murfin tukunyar?