Ga wani dabaran yadda ake dambun nama ya yi kamar auduga sannan ga dadi da kuma sauki. Cikin kalilan lokaci, uwargida zaki hada komai.
Abubuwan hadawa
- Nama
- Albasa
- Attarugu
- Curry
- Maggie
- Onga chicken and classic
- Thyme kadan
- Tafarnuwa
- Gishiri
- Sai wasu spices da seasonings da ki ke so
Yadda ake hadawa
- Ki samu tukunya ki sa nama, albasa, curry, garlic ki jajjaga ki zuba, thyme, gishiri, attarugu, spice da seasoning da ki ke so sai ruwa kadan, ki rufe ki bari namar ta nuna sosai har sai ya ragargaje da kansa.
- Bayan ya nuna sai ki daura wata tukunyar daban akan wuta, ki zuba namar ta ki a ciki, ki samu muciya kiyita juyawa, kina juyawa za ki ga namar na rarrabewa, nama masu kashi ma za ki ga suna barin jikin namar.
- Haka za ki ta yi har sai namar ta bushe ta baki golden brown colour sai ki sauke.
Karin bayani
- Kar ki cika wuta.
- In tukunyar ki kasar ta kama toh ki nemi wata roba ki juya dambun sai ki kankare cikin tukunyar sannan ki sake zubawa ki ci gaba da tukawa.
- In itace ki ke amfani da shi kada ki bari ya yi hayaki dan tiririn zai kama dambun ki.
- Ki kula kada ki cika maggie da gishiri in tayi yawa dambu bata dadi.
Photo credit: Funke Koleosho BlogSpot
Thank