Ku koyi yadda ake farfesun kifi. Wannan farfesun kifi yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Kifi danye
- Maggi 5
- Albasa 1
- Attarugu 4
- Cittah
- Tafarnuwa
Yadda ake hadawa
- Da farko zaki wanke kifinki ki cire dattin sannan ki yanka gunduwa gunduwa.
- Sai ki zuba a tukunyarki ki yanka albasa sannan ki daka attarugu da citta da tafarnuwa ki zuba.
- Sannan sai ki sa maggi da ruwa sai ki rufe ki dora a wuta ki barshi ya nuna. Za ki ji gida ya dau kamshi.
- Idan yayi sai ki sauke ki zuba wa maigida da yara.