Skip to content

Yadda ake cream caramel

Share |
Yadda ake cream caramel
Add to Lists (0)

No account yet? Register

Ga yadda ake cream caramel mu koya ‘yanuwa. Wannan recipe ne mai sauki da kuma dadi cikin ‘yan lokaci kadan za a hada.

Abubuwan hadawa

  1. Kwai uku
  2. Madaran ruwa gwangwani daya (peak milk)
  3. Suga
  4. Filebo

Yadda ake hadawa

  1. Ki fasa kwanki ki sa suga cokali 5, ki juye madara gwangwani daya da filebo ki motsa su hade da juna ki a jiye a gefe.
  2. Ki debo wani sugar ki hada da ruwa da kauri ki daura kan wuta ya narke har ya canza kala ya koma brown.
  3. Sai ki samo container wanda za ki iya sa wa a tukunya, ki sa a cikin tafasashshen ruwa baiyi komi ba,sai ki juye narkakken sugan  a ciki sannan ki kawo hadin madara da kwannan ki zuba a ciki.
  4. Sai ki sa container cikin tukunya mai ruwan kada ya wuce rabin container din ki daura a wuta ya yi ta tafarfasa har abin cikin container yayi kauri.
  5. In ya kame jikin sa ta ko ina, sai ki ciro ki bari ya huce sannan sai ki samo plate ki kifa a kai.
  6. Sai a sa a fridge ya yi sanyi. A ci dadi lafiya. Banason na misalta dadinsa, ku dai ku gwada ku gane wa idanun ku.

Wani abin dadin:

In kina da oven za ki iya sawa a abin gashin cake ki gasa  a ciki, cikin sauki. Dan Allah ku gwada sannan ku bimu da dukkanin ma’aikatan Bakandamiya  da addu’a.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×