Ku koyi yadda ake couscous jollof cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi sha uku da kuma steps hudu.
Abubuwan hadawa
- Couscous
- Tarugu
- Karas
- Maggi
- Kayan kamshi
- Peas
- Koren wake
- Cucumber
- Tsokar kifi
- Masarar gwangwani
- Gishiri
- Albasa
- Daddawa
Yadda ake hadawa
- Daura tukunya a kan wuta ki sa mai sai ki kawo tarugunki ki sa ki kawo albasa ki sa ki soya sama sama sannan ki kawo kayan kamshi, da daddawa ki sa da maggi, da gishiri (iya da zai miki) sai ki soya sama sama.
- Sannan sai ki kawo tsokar kifin ki ki sa ki juya sannan ki kawo tafashashshen ruwa ki sa (ruwan iya wanda zai dafa miki couscous na ki) sai ki juya ki rufe tukunya ki nadan wani lokaci.
- Da zarar kinga ya fara watsartsara sai ki kawo couscous na ki ki zuba a ciki ki rufe tukunya ki, sannan ki rage wuta sosai nadan wani lokaci.
- Daga karshe, sai ki kawo su koren wake, karas (kin dan basu tsoro da ruwan zafi, sannan a ruwan zafi ki sa baking powder), sai ki kawo masarar gwangwani (itama ki tsane ruwan da ke jikin ta kafin kisa) sai ki juya a hankali ki barsu sudan turara a ciki sai ki sauke. A ci dadi lafiya.
Nice👌
Girke girke