Skip to content

Yadda ake cookies

Share |
yadda ake cookies
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake cookies cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi shida da kuma steps biyar.

Abubuwan hadawa

  1. Flour kofi 2
  2. Icing sugar kofi ¾
  3. Butter ½ kofi
  4. Flavor cokali 2 (2stpn)
  5. Kwanduwar 1
  6. Baking powder

Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki tankade flour ki sa baking powder a ciki sai ki ajiye a gefe. Dauko hand mixer ki zuba butter a ciki buga ya bugu sosai sai ki kawo icing sugar ki sa a ciki shima ki buga shi sosai har sai kinga ya yi tashi.
  2. Sai ki kawo kwanduwar kwanki ki sa a ciki ki buga kamar na second 30. Sai ki dauko flavour cokali 2 stpn ki juya su hade da juna.
  3. Sai ki kawo tankadadiyar flour ki ki sa a ciki ki juya a hankali har sai ya hade jikinsa. Sai ki kwashe hadin flour ki sa akan teburi (table) ki yi ta hada shi har sai ya hade ya dungule gu daya sai ki raba shi gida biyu.
  4. Kin sake mulmula shi har sai ya baki dogo kamar sanda sai ki sa folk (cokali mai yatsu) ki na jan layi a jikin sa sai ki sa wukanki ki yanyanka shi ko kuma za ki iya samun kwalba ko rolling pin na ki ki yi rolling na shi ya zama fale fale, ki sa abun yanka cookies ki yanka shi irin yankan da ki ke so.
  5. Sai ki sa a magasa (preheated oven) sai ki gasa har sai ya gasu. Sai ki sauke ya sha iska. Ki sa a plate, sannan za ki iya yaryada nutella a kai. Aci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×