Skip to content

Yadda ake coconut jollof rice

Share |
Yadda ake coconut jollof rice
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Mu koyi yadda ake coconut jollof rice cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Uwargida ki gwada ki zo ki bamu labari. Wai sai an gwada…

Abubuwan hadawa

  1. Tafasashshen shinkafa
  2. Tarugu
  3. Tattasai
  4. Albasa
  5. Tumatur (ki markada)
  6. Karas (yanka shi dogo dogo)
  7. Madarar kwakwa
  8. Dafaffafen kifi (Titus iya tsokar za ki yi amfani da shi )
  9. Kayan kamshi
  10. Maggi
  11. Gishiri kadan
  12. Tumatur na gwangwani
  13. Cucumber (ki yanka)
  14. Kabeji (ki yanka)
  15. Ruwan silalen kifi
  16. Man gyada
  17. Albasa (ki yanka)

Yadda ake hadawa

  1. Ki daura tukunya kin akan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama, sai ki kawo kayan miyanki (tarugu, tattasai, tumatur da albasa) wanda ki ka markada ki sa a cikin tukunyan ki juya sai ki bar shi nadan wani lokaci (ruwan kayan miyan ya shanye).
  2. In ya shanye, sai ki kawo tumatur na gwangwani ki sa a ciki ki juya ki soya sama sama. Sai ki kawo ruwan silalenki kifi ki sa sannan ki kawo madarar kwakwanki ki sa a ciki sannan ki tsaida ruwa kadan (ruwan daidai wanda zai karasa dafa miki shinkafa ki zaki sa).
  3. Kawo kayan kamshi da gishiri kadan da maggi ki sa a ciki (iya dandano da zai mi ki) ki sa ki juya ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin kadan har sai ruwan ya fara tafasa.
  4. Sai ki dauko tafasashshiyar shinkafanki ki zuba sai ki juya ki kara albasa, kifi (iya tsokan za kiyi amfani da shi) ki sa a ciki ki juya, ki rufa mashi leda a kai sai ki dauko murfin tukunya ki rufe na dan wani lokaci har sai ruwan ya kusan shanyewa.
  5. A nan sai ki kawo karas da kabejin ki ki sa ki juya ki rufe tukunya ki na dan wani lokacin kadan ya turaru. Daga karshe sai ki sauke ki sa a plate ki kawo kabeji, cucumber da soyayyen kifi ki sa a gefen shinkafan. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

2 thoughts on “Yadda ake coconut jollof rice”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×