Skip to content

Yadda ake chocolate cake

Share |
Yadda ake chocolate cake
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku karanta yadda ake chocolate cake ta hanyar bin matakai hudu kacal. Wannan recipe ne mai saukin bi da muka bayanai tiryan-tiryan.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi biyu
  2. Rabin butter
  3. Kwai takwas
  4. Sugar Kofi daya
  5. Cocoa powder kofi daya
  6. Butter milk kofi daya
  7. Baking powder karamar cokali daya
  8. Nescafe daya (irin na sachet dinnan)
  9. Chocolate brownie colouring babban cokali biyu in kina dashi
  10. Vanilla flavour karamar cokali daya
  11. Vinegar babban cokali daya in kina dashi

Yadda ake hadawa

  1. Ki sa filawa, baking powder, cocoa powder a roba ki yi mixing na su sai ki ajiye a gefe.
  2. Ki dauko wata roban din ki sa butter da sugar ki yi mixing na su in ya zama fluffy sai ki sa kwai ki juya su hade, sai ki dauko filawa mixture can ki na zubawa ki na mixing harya kare.
  3. Ki zuba 1 strip nescafe a cikin butter milk ki juya sai ki zuba akan kwabin na ki, ki sa vanilla flavour, vinegar, dark chocolate brownie colouring ki juya su hade.
  4. Sai ki dauko pan ki sa cupcake papers, ki zuzzuba. Ki yi preheating oven, in ya yi sai ki sa ki gasa.

Karin bayani

  1. In bakida butter milk ki samu madarar gari 5 tbsp da vinegar ko white ko apple cider 1 tsp ki sa ruwa ki dama 1 cup sai ki yi amfani da shi
  2. In kina so chocolate na ki ya yi moist kada ki cika masa wutan sama .
  3. Bayan kin cire ki bari ya sha iska kadan sai ki samu kwano ki zuba in ba a lokacin za a ci ba.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake chocolate cake”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×