Chinese rice wato shinkafar Sin, wata irin abincin ne da ake samu a ƙasar China, tana daga cikin shahararrun abinci a duniya. Wannan shinkafa yawanci ana soyawa ko haɗa ta da kayan lambu, nama, ƙwai, da kayan yaji na musamman domin ƙara ɗanɗano da ƙamshi.
Akwai nau’ukan girke-girke da dama wanda suke da alaka da chinese rice kamar su fried rice, vegetable rice da, chicken fried rice da egg fried rice.
Abubuwan hadawa
- Dafaffafiyar shinkafa (wanda aka dafa da gishiri)
- Karas (carrots)
- Peas (na gwangwani)
- Albasa
- Kwai
- Tattasai
- Butter
- Gishiri
Yadda ake hadawa
Ku koyi yadda ake Chinese rice ta hanyar bin steps dinnan masu sauki
- Da farko za ki fasa kwanki a ciki wani karamin kwano sai ki yanka mishi albasa, sai ki sa gishiri kadan sannan ki ajiye a gefe.
- Ki yanka su tattasai, albasa kanana, sai ki yanka karas na ki (ki sa masa tafasashshe ruwan zafi da baking powder ki rufe nadan wani lokaci sannan ki tace).
- Ki bude peas naki na gwangwani ki juye shi a kwano sai ki zuba mishi ruwa sosai sannan ki tace. Anan sai ki hada duk veggies naki dukka wuri daya ki ajiye a gefe.
- Ki daura non stick pan naki akan wuta ki sa butter ki a ciki idan ya narke sai ki kawo kwanki ki sa a ciki, sai ki rika juyawa, (kamar yadda ake miyar kwai)
- Idan yayi sai ki dauko su carrot da ki ka gyara ki ka ajiye su wuri daya sai ki zuba a ciki ki juya a hankali dan karya kama.
- Sai ki dauko dafaffafiyar shinkafa ki sa a ciki ki juya a hankali har sai ya yi.
- Sai ki sauke ki sa a plate ki kawo miyar stew ki sa.
Aci lafiya!

