Chicken biryani abinci ne na kasar waje (Indiyawa da Larabawa) wanda ya kunshi spices kala-kala masu inganta lafiya. Protein da carbohydrate ne saboda kaza da shinkafar da ake amfani da su. Mafi yawanci an fi amfani da basmati wurin yi saboda ita ce shinkafar waje, kuma wacce har masu diabetes za su iya ci. Amma babu laifi don an yi amfani da duk shinkafar da ake da ita.
Abubuwan bukata
- 8 pieces chicken parts
- 3 cups basmati rice
- 3 tomatoes
- 1/3 cup unsweetened yoghurt
- 4 tablespoons maggi powder
- 1 teaspoon sea salt
- 1 teaspoon cumin
- 5 green cardamom
- 1 stick cinnamon
- 2 star anise
- 1 tablespoon paprika
- 1 tablespoon chili flakes
- 25cl vegetable oil
- 3 bay leaves
- 1 teaspoon coriander seeds
- 1 teaspoon black pepper corn
- 5 cloves
- 5 white pepper corn
- 1 tablespoon biryani masala
- 1/2 lemon juice+ 1 dried lemon
- drop of yellow food colour or turmeric
- 1 cup caramelized onion
Yadda ake yi
1. ki zuba cumin, black pepper, sea salt, kanumfari, white pepper, da coriander a turmi ki daka su zama gari. (Half na wanda na lissafa a ingredients.
2. sai ki juye su a kan kazarki wadda kika wanke tas kika zuba ta a cikin tukunyarki non stick pots wadda ba ta kamu.

3. Sai ki zuba paprika, chili flakes, da kuma seasoning (shi ma seasoning din half).

4. Ki zuba biryani masala, vegetable oil, yankakken tumatur, yoghurt, then ki yi squeezing lemon juice.

6. Ki saka hannu ki murtsuka sosai sannan ki rufe tukunyar ki bar shi sai bayan awa biyu ko uku.

7. A gefe guda kuma, za ki zuba ruwa a tukunya, ki zuba ragowar spices dinki, da mai da seasoning. Sannan ki zuba vegetable oil. Ki wanke shinkafa ki tsane ta daga ruwa ita ma ki zuba a ciki. Ki bari ta yi 80% cooked sai ki tsane ta a cikin kwando.

8. Ki dora naman nan a kan wuta, sai ki zuba caramelized onion. Sannan ki rufe ki bari ta dahu na minti ashirin a low heat.

9. Ga shi nan bayan naman ya nuna. Ba a kara masa ruwa kwata-kwata. Amma idan kazarki mai karfi ce kika ga ta tsotse ruwan duka to za ki iya kara kadan.

10. Ki raba ta gida biyu ki cire rabin a wani bowl ki bar rabin a cikin tukunya.

11. Ki zuba shinkafar nan a cikin tukunya, amma ba duka ba rabinta za ki zuba. Sai ki juye ragowar naman nan da kika fitar, sai ki barbada caramelized onion, sannan ki karasa juye sauran shinkafar a kai.

12. Ki samu yellow food colour dinki ki jika a ruwa kadan, sai ki saka curry ko turmeric shi ma kadan. Ki barbada a kan shinkafar.

13. Sai ki rufe tukunyar ruf da foil paper ko kuma kitchen towel. Da wuta low ta dahu na minti goma sha biyar.

14. A hankali ki dago shinkafar tun daga kasa amma kar ki yi yadda kalolin biyu za su hade. Shi ke nan sai ki sauke.

15. Ki yi serving a cikin kyakkyawan tray irin na Bakandamiya shopping.
