Skip to content

Yadda ake cheese toast bread

Share |
Yadda ake cheese toast bread
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku karanta yadda ake cheese toast bread. Za ku bi matakai hudu ne masu saukin bi domin gwada wannan recipe. San an gwada…

Abubuwan hadawa

  1. Biredi mai yanka (sliced bread)
  2. Cheese
  3. Butter ko man gyada
  4. Tsokar kaza
  5. Tarugu
  6. Koren tattasai
  7. Karas
  8. Kwai dafaffafe (ki yanka kanana)
  9. Albasa
  10. Lawashi
  11. Maggi
  12. Kayan kamshi kadan

Yadda ake hadawa

  1. Da farko dauko kwano ki hada dafaffafen tsokar kaza ki ki sa maggi iya dandano da zai mi ki, gishiri kadan, kayan kamshi, dafaffen kwai, karas, koren tattasai, albasa duk hada su gu daya ki gauraya ajiye a gefe.
  2. Dauko biredinki mai yanka shafa mishi butter a jikin (amma gefe daya zaki shafa butter) ajiye a gefe shima.
  3. Dauko yankakken biredin dayan daga ciki wanda ki ka shafa masa butter ki shinfida ki kawo kayan hadinki na naman kaza ki sa sai ki dauko cheese ki sa a sama ki sake dauko biredin daya daga cikin wanda ki ka shafa masa butter ki rufa akai ajiye agefe . Haka za ki yi har sai kin gama da sauran biredi ki.
  4. Daga karshe, daura non stick pan akan wuta idan ya yi zafi sai ki dauko biredinki ki na gasawa ki na juyawa (don dukka gefe 2 su gasu) sai ki sauke ki sa a plate. A ci dadi lafiya.

Karin bayani

Za ki iya bawa hadin kazanki tsoro akan wuta kafin ki sa a cikin biredin idan kina so (amma kidan sa butter ko man gyada kadan a ciki).

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake cheese toast bread”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×