Skip to content

Yadda ake chapati da miyar dankali

Share |
Yadda ake chapati da miyar dankali
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake chapati da miyar dankali. Wannan recipe na complete meal wadda idan uwargida ta gwada za ta zo ta bamu labari!

Chapatti:

Abubuwan hadawa

  • Filawa kofi 2
  • Baking powder cokali 1
  • Butter cokali uku (tbsp)
  • Koyi 1
  • Gishiri
  • Ruwa

Yadda ake hadawa

  1. Ki samu kwano mai zurfi (bowl) ki sa filawa (flour), da baking powder, da butter, da koyi, gishiri, ki juya komai ya hade sai ki sa ruwa ki kwaba dough din.
  2. Bayan kin gama kwabawa, sai ki rufe ki bashi irin minti 10 zuwa 15 a rufe. Bayan minti 10 ko 15 din sai ki ciro ki yanka shi zuwa kamar gida takwas (8) sai ki murza shi ya yi dai dai da girma da kuma kaurin da ki ke so.
  3. Ki daura pan a wuta ki gasa akai. Lokacin da kefen farkon ya yi sai ki juya dayan gefen ya gasu shi ma. Idan ba a lokacin za ki ci ba, ki nemi foodflakes ki zuba a ciki ki rufe.

Sannan kar ki cika mi shi wuta da yawa gun gasawa.

Miyar dankali:

Abubuwan hadawa

  • Nama
  • Mai
  • Albasa
  • Tomatur
  • Tattasai
  • Maggi
  • Gishiri
  • Tumeric
  • Ruwa
  • Dankali

Yadda ake hadawa

  1. Ki sami tukunyanki ki daura a wuta ki sa nama (na yi amfani da danyar nama shi ya sa na fara tafasa shi).
  2. Bayan ya tafasa ruwan ya shanye, sai ki zuba mai, da albasa, da tomatur, tattashe, sai ki soya, in ya soyu ki sa maggi, da gishiri, da tumeric, sannan ruwa ki. Ki bari miyar ya danyi kauri, kayan miya su narke.
  3. Bayan miyan ya yi kaurin da ki ke bukata, sai ki zuba dankalinki da ki ka rigaya ki ka yanka in cubes (anan inda bukatar kara ruwa sai ki kara). Shikenan sai ki rufe ki bari ya nuna. Bayan dankalin ya nuna za ki ga ya yi kauri, sannan ya yi kyau komi ya hadu a jikinsa. Sai ki sauke.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×