Uwargida ga yadda ake carrot and orange juice cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi biyar da kuma steps hudu.
Abubuwan hadawa
- Karas
- Lemun zaki (orange)
- Danyar citta
- Sugar
- Ruwa
Yadda ake hadawa
- ki samu karas madaidaici guda biyu, citta karama guda daya ki bare ki yanka su kanana.
- Sai lemu guda biyu, ki bare ki cire ‘ya’yan, itama ki yanka kanana.
- Ki dauko blender ki zuba su duka, ki sa ruwa ki yi blending, in ya yi sai ki kashe ki tace.
- Sugar kuma ki zuba a tukunya ya dan narke ya zama syrup sai ki sa ruwa a kai ki zuba a kan juice din.
Karin bayani
In ki na so ba sai kinyi syrup ba za ki iya sa sugan haka.