Ku koyi yadda ake cabbage jollof rice. Wannan jollof rice ce mai rai da motsi. Idan an gwada a zo a bamu labari.
Abubuwan hadawa
- Tafashashshen shinkafa
- Kifi (ki dafa, ki bare, ki cire qaya)
- Kabeje (ki yanka, ki wanke, ki tsane)
- Albasa (ki yanka)
- Dafaffen kwai (ki yanka kanana)
- Tarugu (ki jajjaga)
- Kayan kamshi
- Daddawa (mai kyau)
- Maggi
- Mai
- Gishiri kadan
Yadda ake hadawa
- Dauko kabeji ki yanka, ki yanka albasa a kai sannan ki sa vinegar ki wanke sai ki tsane a matsani. Ajiye a gefe.
- Daura tukunya, ki sa mai ki kawo albasa tarugu da daddawa, da kayan kamshi, da gishiri da maggi iya dandanon da zai mi ki ki sa, ki juya ki soya sama sama.
- Sai ki tsaida ruwa kamar kofi biyu. Ki bar shi ya yi ta tafasa har sai ya hade jikinsa. Ki bari har sai ruwan ya yi daidai yadda zai karasa miki dafa shinkafanki.
- Ki bar shi ya tafaso sannan ki kawo shinkafarki ki sa, ki kawo kifi da kwanki ki sa sai ki juya, ki rufe ta har sai ruwan ya shanye sai ki kawo kabejin ki wanda ki ka yanka ki sa ki juya a hankali sai ki rufe, su turaru sai ki sauke ki sa a plate.
- Za ki iya kara yanka latas ko kabejin ko ki yanka tomatur a kai. A ci dadi lafiya.