Skip to content

Yadda ake butter icing

Share |
yadda ake butter icing
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku karanta yadda ake butter icing cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi biyar da kuma steps uku.

Abubuwan hadawa

  1. Butter cokali 6
  2. Icing sugar kofi 2
  3. Vanilla flavour cokali 1
  4. Madara ta ruwa cokali 4-6 (tsp)
  5. Piping bag

Yadda ake hadawa

  1. Ki sami mixer machine na ki, ki sa butter a cikin wannan kwanon na shi sai ki kunna shi ya yi ta juyawa har sai butter ki ya fara haske.
  2. Sai ki kawo icing sugar ki sa ki yi ta juyawa, har sai kinga ya yi lumuy. Sannan ki kawo madara da vanilla flavour ki zuba a ciki ki juya har sai ya hade jikinsa.
  3. Daga karshe, sai ki dauko piping bag (dama kin sa mi shi irin bakin adon da ki ke so) ki sa butter a ciki sai ki na matsawa akan cake, cookies da dai sauransu. Ki yi irin adon da ki ke so.

Karin bayani

Za ki iya sa mi shi colour da ki ke so kafin ki sa a leda (piping bag).

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×