Skip to content

Yadda ake burger a gida

Share |
Yadda ake burger a gida
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake burger a gida mai dadi. Wannan burger ce ta gida gangariya wadda za a ci hankali kwance domin duk abinda ke ciki an sani!

Abubuwan hadawa

  • Filawa kofi daya
  • Yeast cokali 1(tsp)
  • Madarar gari (powdered milk) cokali 2(tbsp)
  • Gishiri dan kadan
  • Ruwa mai dumi

Yadda ake hada beredin

  1. Ki samu kwano mai zurfi (bowl) ki sa filawa, da yeast, da powdered milk, sai gishiri da ruwa mai dumi ki dama sai ki raba dough din kashi uku ko hudu ki yi making ballsm.
  2. Ki samu pan ki shafa butter ko mai ki jera dough in kibarshi na kamar minti 30 ya ta shi sai ki yi preheating oven ki sa ki gasa.
  3. Bayan kin gasa yadan sha iska sai ki yanka bread din ta gefe zuwa kasha biyu (ya baki half circles biyu ke nan).

Fillings da hada burger din:

Abubuwan hadawa

  • Minced meat(dakaken nama)
  • Albasa kadan
  • Maggi
  • Attarugu
  • Tomatur
  • Lettuce (salad)
  • Koren tattasai (green bell pepper)
  • Sausage in kina so
  • Cheddar cheese (ba dole ba)
  • Kwai 1
  • Mai kadan

Yadda ake hadawa

  1. Ki samu kwano mai zurfi (bowl) ki zuba minced meat, yankakken albasa (chopped onion), da attarugu, da maggi, kwai daya.Sai ki hadasu su hadu, sai ki su kwalo kwallo (making into balls), sannan ki rika dannawa da tafin hannu ya dan yi flat kadan.
  2. Ki daura pan a wuta ki sa mai kadan ki soya sai ki ajiye a gefe
  3. Ki soya wata kwai daban kamar omelette, sannan ki ajiye a gefe. Ki samu sausage ki dan soya sama sama a pan sai ki yanka ta dogo dogo.
  4. In kin kare sai ki dauko bread na ki, ki fara saka cheddar cheese, yankakken tumatir (sliced tomato), da lettuce, da sliced onion, da koren tattasai (green bell pepper), da sausage, sannan da omelette, zuwa minced meat da kika soya, sannan sai wata omellette din sai ki kifa rabin bread din akai. Ki shafa mai kadan a pan sai ki daura bread din akai amma wutar ki ya zama ya na kasa sosai (low heat) in cheddar cheese ya dan narke sai ki sauke. Shike nan burger ya hadu sai ci.

Karin bayani

In ba ki sa cheddar cheese ba babu bukatar daura a pan bayan kinsa fillings dinky.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×