Mu koyi yadda ake bread bowls cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Uwargida ki gwada ki zo ki bamu labari. Wai sai an gwada…
Abubuwan hadawa
- Bread mai yanka
- Dafaffen nama
- Tarugu
- Abasa
- Butter
- Kabeji
- Maggi
- Kayan kamshi
- Albasa
- Lawashi
Yadda ake hadawa
- Dauko pan na ki ki sa a wuta sai ki sa butter kadan ki yanka albasa ki soya sama sama, sai ki kawo nama ki sa, ki juya shi dauko tarugu ki sa, maggi iya dandano da zai mi ki saka ki juya, kayan kamshi ki sa a ciki sai ki juya ki sa ruwan zafi ko silale a ciki ki juya ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye sai ki bude ki sa kabejin a ciki ki juya kidan barshi ya turaru kadan sai ki sauke, ajiye a gefe.
- Ki dauko bread mai yanka ki yanke gefen gefen jiki (ki yi trimming edges din) ajiye a gefe.
- Dauko bread na ki (wanda ki kayi yanke gefen gefen) ki sa kwalba ko rolling pin Ki murza har sai ya yi fale fale sai ki dauko kanana abun gasa cupcakes ki shafa butter a jikin abun (muffin pan) sai ki na sa breadinki a ciki (ki na manna wa a jiki yanda zai baki rami a tsakiya).
- Sai ki dauko hadin nama da kabejinki ki sa ki cike ramin nan da shi
- Daga karshe sai ki sa a oven ki gasa kamar minti 3-6 (ya danganta da irin yadda ki ke gasuwanki), sai ki sauke ki sa a plate.