Skip to content

Yadda ake beef wraps

Share
Yadda ake beef wraps
4.5
(2)
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku shirya tsaf dan ganin yadda ake beef wraps da zallar tsokar nama. A yau mun zo muku da wani salon sarrafa nikakken nama a nade shi a gurasar larabawa. Ga yadda za mu hada shi cikin sauki da kuma armashi.

Abubuwan hadawa

1. Albasa

2. Nikakken nama (son samu a nika shi da mint leaves da persley)

3. Cheese (optional )

4. Green pepper

5. Kayan dandano

6. Spices

7. Labanese bread

8. Mayonnaise

Yadda ake hadawa

1. Da farko za ki daura frying pan, kisa mai kadan kisa albasa ya soyu ya yi ja.

2. Sai ki kawo nikakken naman ki zuba hade da kayan kamshi da kayan dandano kisa

3. Sai ki barshi har ruwan jikinsa ya fito ya tsotse. Ki kawo green beans da danyar albasa kisa, ki dan juya kadan su dan yi laushi sai ki sauke.

4. Daga nan sai ki dauko labanese bread dinki ki shinfide, ki shafe da mayonnaise kisa naman, sai ki yaryada cheese a saman naman, sai ki kalmashe shi ta gefe yadda zai baki shape kaman na yadda ake meat pie ko half circle D.

5. Sai a daura abun suyan kwai yai zafi asa gefe daya, idan ya gasu a juya dayan gefen.

Shi kenan kin gama beef wraps dinki, sai ayi serving dinsa da tea ko soft drinks.

How many stars will you give this recipe?

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page