Ku koyi yadda ake beef samosa, meat pie, spring roll filling. Wannan filling na gama gari ne domin samosa, meat pie ko spring roll.
Abubuwan hadawa
- Dafaffen nama (daka a turmi)
- Tarugu (ki jajjaga)
- Karas (ki yanka kanana)
- Koren wake (ki yanka kanana)
- Albasa (ki yanka)
- Kayan kamshi
- Maggi
Yadda ake hadawa
- Da farko ki daura kasko ko tukunya akan wuta, ki zuba mai kadan, kawo tarugu, ki sa albasa, ki hada sai ki juya.
- Kawo nama (wanda aka riga aka daka a turmi) ki sa a ciki sai ki yayyafa ruwa kadan a kai.
- Ki kawo maggi da kayan kamshi ki sa ki juya. Ki rufe ki bar shi nadan wani lokaci. Ki rage wuta.
- Daga karshe, ki kawo koren wake da karas ki sa ki juya ki rufe, su dan turara a ciki sai ki sauke. Wannan filling za ki iya yin samosa, ko meat pie da dai sauransu da shi.