Ku koyi yadda ake beef samosa, meat pie, spring roll filling. Wannan filling na gama gari ne domin samosa, meat pie ko spring roll.
Abubuwan hadawa
- Dafaffen nama (daka a turmi)
- Tarugu (ki jajjaga)
- Karas (ki yanka kanana)
- Koren wake (ki yanka kanana)
- Albasa (ki yanka)
- Kayan kamshi
- Maggi
Yadda ake hadawa
- Da farko ki daura kasko ko tukunya akan wuta, ki zuba mai kadan, kawo tarugu, ki sa albasa, ki hada sai ki juya.
- Kawo nama (wanda aka riga aka daka a turmi) ki sa a ciki sai ki yayyafa ruwa kadan a kai.
- Ki kawo maggi da kayan kamshi ki sa ki juya. Ki rufe ki bar shi nadan wani lokaci. Ki rage wuta.
- Daga karshe, ki kawo koren wake da karas ki sa ki juya ki rufe, su dan turara a ciki sai ki sauke. Wannan filling za ki iya yin samosa, ko meat pie da dai sauransu da shi.
Assalamu alaikum ,gaskiya muna karuwa da girke girke ,Allah yara basira, sannan ada INA cikin wannan page na Bakandamiya,amma tunda na canza ways,nasake download din wani app din ,sai nakasa shiga nayi nayi har yanzu.
Waalaikum salam
Amin. Mun gode da addu’anki. Yanzu wancan app din ba ya aiki. Amma za ki iya shiga ta browser a bakandamiya.com. Domin girke-girke kuma wannan website din ne, wato girke-girke.bakandamiya.com. Sannan idan kuma labarun novels ne zalla to ki duba hikaya.bakandamiya.com.