Mu koyi yadda ake basise cikin sauki. Kayan hadi guda biyar kawai ake bukata, da kuma matakai guda biyu domin hada wannan recipe.
Abubuwan hadawa
- Shinkafar tuwo
- Madarar gari
- Citta
- Mai
- Suga
Yadda ake hadawa
1.Za ki dafa shinkafar tuwo da sugar a ciki sai ta yi lub ta zo karshe sai ki dama madara ki zuba
2. Ki rufe ki bari na minti daya sai ki kwashe ki kawo mai ki dan zuba a kai, Shikenan Basisenki ta hadu.
Ana iya shan basise da sanyi wato bayan kinsa a fridge ko kin bari ya huce. Ana kuma iya sha da zafi. Za ki iya yi masa kwalliya da duk kayan marmari da kike so. Nakan yi wa nawa dai kwalliya ne da koriyar tuffa da kuma jan tuffa sai kuma jan inabi.