Skip to content

Yadda ake banana pancake

yadda ake banana pancake
0
(0)

Pancake yana daya daga cikin snacks masu saukin yi, ana yi wa yara domin zuwa makaranta, sannan ana yin shi domin karin kumallo. A yau na zo maku ne da yadda ake yin pancake mai ayaba.

Abubuwan bukata:

1- 1 cup flour

2- 2 eggs

3- 2 bananas

4- 1/2 teaspoon cinnamon powder

5- 1/2 teaspoon baking powder

6- 1/4 teaspoon baking soda

7- 1/2 teaspoon salt

8- 3 tablespoons sugar

9- 1 teaspoon vanilla flavor

10- 1 cup liquid milk

Yadda ake yi:

1- Wannan su ne ingredients dinmu.

yadda ake banana pancake 1

2- ki fara zuba ayaba a cikin mixing bowl, sai ki mashing dinta da masher irin ta Bakandamiya shopping, ko kuma fork mai kyau har sai ta dame. Sai ki zuba madara da flavor ki motsa. Ki dora rariya a kai ki zuba flour.

yadda ake banana pancake 2

2- ki zuba ragowar duka dry ingredients dinki ki tankade ki motsa da kyau.

yadda ake banana pancake 3

3- a wani bowl din daban, ki fasa kwai ki zuba sugar sai ki amfani da hand whisk ko kuma mixer ki ta mixing dinsa har sai ya yi kumfa sosai.

yadda ake banana shopping 4

4- sai ki juye wannan egg mixture din a kan wancan kwabin da kika yi na farko. Ki yi folding da silicon spatula.

yadda ake banana pancake 5

5- ki samu pan dinki mai kyau ko kuma non stick frying pan. Ki goge da tissue sai ki dinga zubawa kadan. Idan dayan gefen ya yi sai ki juya. Amma ba a son wuta da yawa don kar ya kone.

yadda ake banana pancake 6

6- idan dayan gefen ya yi shi ma sai ki kashe. Haka za ki yi har sai kin gama.

yadda ake banana pancake 7

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×