Skip to content

Yadda ake appetizer salad

Share |
Yadda ake appetizer salad Abubuwan hadawa 1. Latas 2. Cucumber 3. Koriyar tattasai 4. Karsa 5. Tumatir 6. Koiyar tuffa (green apple) 7. Kayan kamsahi (busashshiyar na’a na’a, nikakkiyar habbatussauda, maggi) 8. Mai (idan da hali ki yi amfani da man zaitun) 9. Lemon tsami/khal (vinegar) Yadda ake hadawa 1. Za ki wanke kayan da muka ambato da kyau da gishiri ko ruwan khal sannan kiyayyanka su kanana-kanana ki cakude su kaman yadda ki ka gani a hotonnan. 2. Sai ki samo spices dinki kaman busashshiyar na’a na’a, nikakkiyar habba da maggi ki hade wuri guda, sai ki sa mai da lemon tsami ko khal a ciki. Zai yi kyau sossai in ki ka yi amfani da man zaytun! In ki ka hade su wuri daya sai ki zuba kan salad dinki a cakude a ci! Wannan salad yana da kyau mace mai girki tarika kokarin hadawa da shi saboda yana kunshe ne da abubuwa masu amfani ga jikin dan adam. Wannan salad din na da matukar amfani sannan kuma yana da matukar dadi a baki!
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake appetizer salad cikin sauki. Wannan salad ne mai dadi da kuma ingancin gaske. Uwargida a gwada a bamu labari!

Abubuwan hadawa

  1. Latas
  2. Cucumber
  3. Koriyar tattasai
  4. Karsa
  5. Tumatir
  6. Koiyar tuffa (green apple)
  7. Kayan kamsahi (busashshiyar na’a na’a, nikakkiyar habbatussauda, maggi)
  8. Mai (idan da hali ki yi amfani da man zaitun)
  9. Lemon tsami/khal (vinegar)

Yadda ake hadawa

1. Za ki wanke kayan da muka ambato da kyau da gishiri ko ruwan khal sannan kiyayyanka su kanana-kanana ki cakude su kaman yadda ki ka gani a hotonnan.

2. Sai ki samo spices dinki kaman busashshiyar na’a na’a, nikakkiyar habba da maggi ki hade wuri guda, sai ki sa mai da lemon tsami ko khal a ciki. Zai yi kyau sossai in ki ka yi amfani da man zaytun!

In ki ka hade su wuri daya sai ki zuba kan salad dinki a cakude a ci!

Wannan salad yana da kyau mace mai girki tarika kokarin hadawa da shi saboda yana kunshe ne da abubuwa masu amfani ga jikin dan adam. Wannan salad din na da matukar amfani sannan kuma yana da matukar dadi a baki!  

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×