Albishir wani nau’i ne na local candies wanda ake yin shi da zallar madara. Yana kama da alewar madara sai dai shi yana da danko. Mutane musamman masu sha’awar kayan zaki suna matukar son shi. A yau na zo maku ne da hanya mai sauki wadda ake yin albishir mai dadi.
Abubuwan bukata:
1- 2 and 1/2 cups powdered milk
2- 1 cup sugar
3- 1 tablespoon lemon juice
4- 1 cup extra powdered milk
5- 1/4 cup water
Yadda ake yi:
1- ki zuba sugar a cikin kyakkyawan non stick frying pan dinki. Irin wanda kowace mace ya kamata ta mallake shi, idan ba ki da shi ki duba Bakandamiya shopping ki sayi mai kyau da nagarta.

2- Sai ki zuba ruwa ki kunna wuta medium low flame.

3- Idan sugar din ya fara narkewa sai ki zuba lemon tsami ki bar shi ya yi ta dahuwa har sai ya yi danko sosai ya fara sauya kala

4- Sai ki kawo madararki ki zuba a ciki

5- Ki yi amfani da silicon spatula ki ta motsawa har sai komai ya hade. Za ki gan shi ya yi danko.

6- Sai ki samu parchment paper ki juye a kai yadda ba zai manne ba.

7- Sai ki amfani da rolling pin ki flattening dinsa da fadi.

8- Ki kawo madara ki barbada a sama

9- Ki samu wuka mai kaifi ki yanka daidai girman da kike so.

10- ki tabbata har can kasan ma kin zuba masa madara. Sai ki bari ya huce za ki ga ya dan yi karfi. Sannan ki storing.

