Skip to content

Yadda ake alalen man gyada

Share
Yadda ake alalen man gyada
5
(2)
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ga yadda ake alalen man gyada mu koya ‘yanuwa. Wannan recipe ne da duk masoyin alale da kayan waken zai so ya gwada. Ku gwad ku bani labari.

Abubuwan hadawa 

  1. Wake
  2. Albasa
  3. Tattasai
  4. Attarugu
  5. Crayfish
  6. Man gyada
  7. Maggi star
  8. Gishiri
  9. Citta da tafarnuwa
  10. Ledan alale
  11. Tafasashiyar kwai 

Yadda ake hadawa 

  1. A wanke wake a cire bayansa tsaf.
  2. Ayayyanka albasa a ciki a sa tattasai da tarugu a sa citta da tafarnuwa da crayfish a kai a niko (wurin nikan a ce nikan alale za’ayi)
  3. In an kawo nikan, sai a sa maggi da man gyada a hade ko ina yaji da kyau sai a sa yankakkiyar dafaffiyar kwai a kukkulla a leda.
  4. A sa a tukunya a sa ruwa a daura kan wuta har alalen ya dahu. 

Karin bayani

Yadda za ki gane alalen ya dahu shi ne za ki ga alalen ya bar jikin leda, hakan na nunin cewa alalen ya dahu kenan. 

How many stars will you give this recipe?

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page