Ga yadda ake alalen kifi da kwai mu koya ‘yanuwa. Wannan recipe ne mai dadi kuma cikin ‘yan lokaci kadan uwargida za ki hada komai da komai.
Abubuwan hadawa
- Wake
- Tarugu
- Tattasai
- Albasa
- Manja
- Man gyada
- Kifi ko hanta (dafaffafe)
- Ruwan silalen kifin
- Crayfish (ba dole ba)
- Kwai (dafaffafe )
- Maggi
- Gishiri
Yadda ake hadawa
- Ki dauko wakenki ki surfa, ki wanke ki tabbatar kin cire bawon jikin waken duka.
- Sai ki wanke kayan miyan tare da albasa ki sa akan wakenki a kai nika ko ki sa a blender ki nika a gida.
- Ki dauko dafaffafen kifinkinki ki cire duk wani kaya dake jikinsa ki gutsura sala sala sai ki ajiye a gefe, sannan sai ki dauko dafaffafen kwanki ki yanka shi kanana ki ajiye a gefe shima.
- Dauko markaden waken ki zuba manja da man gyada sai ki bugashi sosai , sannan ki kawo silalen kifinki ki sa a ciki ki bugashi, sannan ki sa maggi (iya dandanon da zai miki), crayfish kadan, gishiri kadan sai ki bugashi sosai, idan kinga ta yi kauri za ki iya kara ruwan dumi a ciki sai ki juya.
- Ki dauko leda ki na diban kulli ki na sawa a ciki ki na daukan kifi da kwan ki na sawa sai ki kulla (idan ki na so kuma za ki iya zuba kifin da kwan a cikin kullin sai ki kulla). Haka za kiyi da sauran kullin har ki gama.
- Bayan kin gama gullawa, sai ki daura tukunyanki akan wuta ki sa ruwa a ciki (ana so kiyi hakan ne kafin ki fara kulla alalenki) idan ya tafasa sai ki dauko alalanki ta leda ki sa a ciki (kafin ki sa ki tabbatar kin jijjagashi ahankali sai ki sa cikin ruwan zafin ki dafa har sai ya nuna.
Za ki iya ci da yaji da manja ko kuma shi kadensa. A ci dadi lafiya