Wannan abinci ne mai matukar dadi, Wanda za ka iya tarbar baki da shi, ko kuma ku yi a gida ku ci. Canjin abinci yana da amfani ba wai kullum ke ce yin dafaduka ko shinkafa da miya ba. Idan hali ya bayar ki gwada yin wannan abincin za ku ji dadinsa a karshe.
Abubuwan bukata:
For the rice
1- 3 cups basmati rice
2- 3 carrots
3- 1/2 red bell pepper
4- 1/2 green bell pepper
5- 1 teaspoon ginger and garlic paste
6- 1/2 onion
7- 1/2 cup vegetable oil
For the soup
1- 1 chicken breast
2- 3 Irish potatoes
3- 2 tablespoons seasoning powder
4- 1 teaspoon ginger and garlic paste
5- 1 tablespoon cornflour
6- 1 teaspoon parsley flakes
7- water as required
8- 1 sachet tomato paste
9- 1 cup pepper mix
10- 1/2 cup oil
11- 1 teaspoon mixed spices
Yadda ake yi
1- ki zuba mai a cikin kyakkyawan wok pan dinki irin na Bakandamiya shopping. Idan ya yi zafi sai ki zuba ginger and garlic da albasa ki soya har sai kin ji kamshinsu ya fara fita. Daga nan sai ki zuba carrot ki soya shi kadan, then ki zuba per boiled rice ki rage wuta.

2- Ki zuba bell pepper dinki ki juya da kyau har sai komai ya garwaye. Sai ki dan yayyafa ruwa ki bari ya turara na akalla minti bakwai zuwa minti goma.

3- Ita kuma miyar za ki zuba mai a cikin pan, ki zuba albasa da ginger and garlic, ki dan soya su sannan ki kawo chicken breast wanda kika yanka size din da kike so ki zuba. Ki dan soya na minti biyar sannan ki kwashe a wani bowl.

4- Ki sake zuba wani mai da cornflour a cikin pan din, ki saka tomato paste da pepper mix a ciki, ki soya su sannan ki zuba irish da kika yanka shi ma size din da kike so da wannan kazar wadda kika kwashe da farko.

5- Ki zuba seasoning and spices yadda zai ji sai ki jujjuya su hade sosai. Then ki zuba makimancin ruwa yadda kika san dai za ki bukata. Ki bari sai sun dahu komai ya yi sai ki zuba parsley flakes amma ba dole ba ne, yana dai kara kamshi da dadi ne.

6- Idan komai ya yi sai ki sauke ki yi serving a cikin kyakkyawan
Plate. Na hada da coleslaw da fried plantains

