Nau’in sunflower yana daga cikin flowers masu kyau da tsarin da ake so. Manya da kananan yara duk suna son kyautarta. Hakan ya sa na kirkiri wannan cookies din domin na burge mutane a ranar da na cika shekara biyar da aure.
Ingredients
1- 1 and 3/4 cups flour
2- 1/4 cup granulated sugar
3- 1/4 cup icing sugar
4- 125g room temperature margarine
5- 1/2 teaspoon flavor
6- 1/2 teaspoon baking powder
7- 1 egg
8- 1 tablespoon cocoa powder
9- Drop of yellow food coloring
10- 1/8 cup liquid milk
Yadda ake yi:
1- Ga ingredients dinmu nan duka. Za ki zuba butter a bowl, sai ki zuba icing da normal sugar ki creaming dinsu da kyau. Sannan ki zuba kwai, madara, da flavor.

3- idan kin yi creaming dinsu sai ki kawo flour da baking powder ki sa. Ki motsa har sai ya zama dough.

4- Sai ki dibi 1/3 na dough din ki saka masa cocoa powder. Ragowar mai yawan kuma ki saka yellow food coloring.

5- ki flattening yellow din sannan ki sa cutter ki fitar da shi. Babban round za ki fara sannan karami shi ne na biyun.

6- Sai ki dora a kan tray ki saka shi cikin fridge na minti goma saboda ya kama jikinsa.

7- Sai ki flattening brown din ma, ki amfani da karamar cutter ki cire sannan ki replacing wancan yellow din na tsakiya da kika cire.

8- sai ki samu cokali wanda yake da sharp edges, ki danna kamar haka.

9- Ki samu skewer ki soka a tsakiyar yadda shape din zai fita da kyau. Daga nan sai ki sa a oven ki gasa da wutar sama da kasa amma medium, na minti goma zuwa sha biyar.

Za ku samu nau’ukan kayan kitchen ko me kuke so a Bakandamiya shopping.