Na san da yawan mutane idan na ce strawberry milkshake abu na farko da za su kawo a ransu shi ne strawberry ake markadawa. Har ma su fara tambayar kansu a ina za su samu strawberry? May be a inda suke yana wahala, ko kuma ba season dinsa ba ne. To ku tsaya ku ji! Hanya ce mai sauki wadda babu ruwanku da neman strawberry. A cikin gidanku ba tare da kun wahala ba za ku hada wannan drink din mai matukar dadi, wanda har business ma za ku iya farawa da shi.
Abubuwan bukata:
1- 2 liters water
2- 1 and 1/2 cups powdered milk
3- 1 cup peak milk powder
4- 7 sachets strawberry cowbell milk
5- 1/2 cup whipping cream/ heavy cream
6- 1/2 cup sugar
7- 1 tablespoon strawberry flavor
Yadda ake yi:
1- Ki samu bowl mai girma, ki zuba madararki ta gari, sannan ki kawo peak ita ma ta gari, sai sugar, heavy cream, da kuma strawberry flavor.

2- Sai ki kawo cowbell dinki ta strawberry ki zuba. Idan ba ki da ita za ki kara adadin flavor da adadin madara. Sannan ki saka pink food colour kadan. Then ki zuba ruwa liter biyu. Ki motsa da kyau.

3- sannan ki samu matacinki mai tsafta ki tace shi saboda za a iya samun abubuwa a ciki musamman kululan madara.

4- sai ki samu bottles dinki masu kyau ki dura a ciki. Da wannan measurement din na samu 25cl guda uku, sai 35cl guda uku.

5- Idan a gida za a sha kuma sai ki samu kyakkywan kofi irin na Bakandamiya shopping ki yi serving a ciki.
