Hanyoyin sarrafa dankali suna da yawa, wasu na soya shi cikin ruwan mai, wasu su dafa tare da nama, wasu su dafa shi zalla, da sauransu. A yau na kawo maku hanya mai sauki mai dadi, sannan babu ruwanki da batun dankali ya sha mai saboda masu ulcer ko wani larurin da ba su son maiko. Wannan dankalin ba ya shan mai ko kadan.
Abubuwan bukata:
1- 1/2 mudu irish potatoes
2- 1 cup all purpose flour
3- 1 teaspoon cornflour
4- 1 teaspoon salt
5- 1 tablespoon mixed spices
6- Oil for frying
Yadda ake yi:
1- Ki fere irish ki wanke ki yanka sizes din da kike so. Sai ki zuba a cikin kyakkyawar sauce pan ki zuba gishiri

2-Ki zuba ruwa ba mai yawa ba

3- Idan ya yi tafasa guda sai ki sauke ki tsame a colander, bayan ya gama tsanewa sai ki sauke ki juye a kitchen towel mai tsafta ki goge dankalin sosai ba a son shi da ruwa ko kadan

4- Daga nan sai ki juye a wata container mai dan girma sai ki zuba flour

5- Then ki saka spices. Na yi amfani da paprika, black pepper, garlic powder, chili flakes, sai gishiri kadan.

6- Ki zakuda da kyau duk su hade

7- Sai ki dora mai a wuta idan ya yi zafi ki zuba dankali ki soya

8- Depending da kalar da kike son shi. Ko golden brown ko golden ko ma dai wane kike so. Ki suba a colander ya karasa tsanewa.

9- Wannan dankalin bai da shan mai ko kadan. Har masu ulcer in shaa Allahu za su iya cin shi ulcer ba ta tashi ba.
