Skip to content

Plantain and egg frittata

Share |
plantain and egg frittata
Add to Lists (0)

No account yet? Register

Ga yadda ake plantain and egg frittata cikin sauki. Wannan recipe na da saurin hadawa ga kuma dadi. Ba a bawa yaro mai kiwuya.

Abubuwan hadawa

 1. Agada (plantain)
 2. Kwai
 3. Sausage ko nama (yanka kanana)
 4. Tarugu (ki jajjaga)
 5. Gishiri kadan
 6. Albasa (ki yanka)
 7. Maggi
 8. Curry
 9. Thyme
 10. Lawashi

Yadda ake hadawa

 1.  Ki dauko agada ki bare bayan ki yanka shi (yanka irin na soyawa).
 2. Sai ki daura kaskonki akan wuta ki sa man gyada idan ya yi zafi sai ki dauko yankakken agadanki ki soya.
 3. Idan ya soyu sai ki tsane a matsani. Ajiye a gefe.
 4. Dauko kwano daban ki fasa kwanki a ciki ki yanka albasa ki sa gishiri kadan da lawashi ki buga shi sosai. Ajiye a gefe.
 5. Daura nonstick pan na ki akan wuta, ki sa mai kadan sai ki yanka albasa ki kawo sausage ki soya sama sama shima, kawo tarugu ki sa ki juya ki kawo maggi, curry da thyme ki sa ki juya ki rage wuta sosai.
 6. Sai ki kawo kwanki (wanda ki ka fasa ki yanka albasa a ciki) ki yaryada har sai ya rufe kan hadinki.
 7. Ki kawo soyayyen agada ki jera akan kwanki sai ki samu murfi ki rufe nadan wani lokaci.
 8. Dauko paranti marar zurfi ki bude marfi nonstick pan na ki sai ki rufa paranti akan non stickpan na ki ki juyo shi sai ki kara mayarwa a cikin nonstick pan din a hankali ki sake rufawa har sai ya gasu sai ki sauke. A ci dadi lafiya 

Karin bayani

Idan baki son ki juya da paranti za ki iya sa nonstick pan na ki a oven dan ya karasa nuna ba sai kin juya shi da paranti ba.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×