Ga wani refreshing drink nan, mai matukar dadi da sanyaya makoshi. Yana da saukin yi, sannan ba za a kashe kudi masu yawa ba idan za a yi shi. Ga duk wanda ga gwada shi zai gode mini.
Abubuwan bukata:
1- 1/2 cup pineapple and ginger juice
2- 1 cup kankara
3- 1 bottle sprite
Yadda ake yi:
1- ki nemi kyakkyawan glass cup dinki, ki zuba pineapple and ginger juice (na markada abarba tare da citta na tace)

2- Sai ki zuba kankara wadatacciya

3- Za ki kusan cika cup din ne saboda idan ya yi sanyi sosai ya fi dadi

4- Sai ki zuba sprite ko kuma 7up. Ki karasa cika cup din da shi.

5- Shi ke nan kin yi kin gama. Sai a sha.
