Cake yana daya daga cikin snacks din da mutane ke so amma kuma yake ba su wahala wurin yi. Tambayoyin da nake yawan amsawa shi ne yaya zan yi cupcake ya yi taushi da dadi? Shin zan iya yin cupcake babu butter? A yau na zo maku da wannan amsar. Ku biyo ni domin ganin yadda ake yin cupcake babu butter kuma ya yi taushi da dadi.
Abubuwan bukata:
1- 3 cups flour
2- 1 and 1/2 cups sugar
3- 2 teaspoons baking powder
4- 1 teaspoon salt
5- 4 eggs
6- 1/2 cup vegetable oil
7- 1 tablespoon vanilla and milk zest flavors
8- 1/4 cup chocolate chips
9- 1 cup liquid milk
Extra
1- 1/2 cup flour
2- 1/2 cup milk powder
3- 2 tablespoons butter
Yadda ake yi:
1- Ki zuba sugar a cikin bowl, sai ki zuba duk wet ingredients din a ciki ki motsa sosai da hand whisk ko mixer har sai kin daina jin karar sugar alamun ya gama narkewa.

2- Sai ki zuba dry ingredients din ma, amma za ki tankade da rariya in case ko akwai wasu abubuwan a cikin flour.

3- Ki zuba chocolate chip din sannan ki motsa ta hade sosai.

4- A wani bowl daban ki zuba flour da madara da butter. Ki murza sai sun zama crumbs. (Wannan steps din duka ba dole ba ne.)

4- Sai ki jera liners a cikin pan, ki dinga zuba wannan cake batter amma kada ya cika taf don zai kumbura idan ya fara gasuwa. Sai ki barbada wannan crumb din a sama, ki kara zuba chocolate chips ma. Amma ba dole sai kin yi mai crumbs din nan ba. Yana dai kara masa dadi.

5- Ga shi nan. already kin yi pre heating oven dinki. Sai ki dauka ki gasa shi da wutar sama kadai, na minti sha biyar zuwa ashirin. Idan ya gasu sai ki kunna wutar sama saboda kalarsa ta yi golden brown.

6- To ga cake nan ya gasu. Shi ke nan an gama.
